Gwamnatin Jihar Sokoto ta kashe sama da naira biliyan biyar wajen aiwatar da shirin cimma muradun karni wato (SDGs) daga shekarar 2019 zuwa yanzu.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin gwamnan Jihar ta Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yayin da ke shaida bikin yayen matasa 1,700 da suka kunshi mata 550 da maza 1,150 da Gwamnatin jihar ta koyar a bangaren sana’o’in dogara da kai daban daban.
Taron wanda shirin SGDs na koyar da matasa sana’o’in ta shekara 2021/2022 ya shirya da hadin guiwar kamfanin Nabilhash, Tambuwal ya ce wadanda aka yaye din an horas da su bangaren sana’o’in daban-daban har guda 12 domin su zama masu tsayuwa da kafafunsu kuma masu amfani a cikin al’umma.
Ya ce, matasan sun samu horo sosai da ilimi kan sana’o’i, wanda hakan ya zama musu kamar wasu sabbin hanyoyi ne na dogoro da kai kuma jihar za ta samu cigaba a sanadiyyarsu.
Tambuwal ya kara da cewa ba wai zallar ma daukan nauyin koyar da matasan suka yi ba, har ma da samar musu da kayayyakin aiki na zamani da za a bai wa kowanne daga cikinsu domin ya cigaba da rike kansa a bangaren sana’ar da ya samu horo a kai.
Daga bisani ya jawo hankalin wadanda suka samu cin gajiyar shirin da su tabbatar sun yi amfani da su yadda kamata domin tabbatar da sun tsayu da kafafunsu.
Ya tabbatar da cewa ta irin wannan shirin za a rage kaifin talauci da fatara sosai a jihar kuma kwalliya har ta fara biyan kudin sabulu