Gwamnatin Jihar Kaduna ta dage dokar hana fita da ta sanya a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniya a karamar hukumar Chikun.
A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a karamar hukumar sakamakon kashe wasu mutane biyu.
- Jami’ar MAAUN Kano Ta Rantsar Da Dalibai 1,200 A Zangon Karatu Na 2022/23
- Firaministan Malaysia: Shawarar Wayewar Kan Kasa Da Kasa Za Ta Taimaka Wajen Tinkatar Matsaloli
Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar ranar Asabar ya ce an cire dokar hana fita.
“An cire dokar hana fita ta sa’o’i 12 da aka kafa a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniya a karamar hukumar Chikun, daga yau Asabar 8 ga watan Afrilu 2023.
“Sojoji da ‘yan sanda za su ci gaba da gudanar da sintiri a wuraren, domin mazauna yankin na iya yin ayyukansu yadda ya kamata a yanzu.
“Gwamnatin ta kuma shawarci ‘yan kasa da su nisanta kansu daga ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, saboda za a magance su nan da nan kamar yadda doka ta tanada,” in ji sanarwar.