Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kashe wasu mutane 15 a wasu hare-haren ‘yan bindiga a kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Kajuru a jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar, gwamnatin jihar ta kuma jajanta wa wadanda harin ya rutsa da su.
- Dalibi Ya Rataye Kansa Har Lahira Saboda Budurwarsa Ta Auri Wani A Gombe
- Nijeriya Na Iya Fuskantar Karancin Abinci A 2023 –IMF
Aruwan ya ce jami’an tsaro sun sanar da gwamnati cewa ‘yan bindiga sun kai hari a Rafin Sarki a karamar hukumar Giwa inda aka tabbatar da kashe mutane 11.
Wadanda aka kashen sun hada da: Abdullahi Musa, Adamu Musa, Aminu Nasiru, Adamu Ibrahim, Ya’u Usman Ladan, Yunusa Saidu, Salisu Abdulrahman, Fati Usman, Yakubu Ya’u, Marwanu Ibrahim da kuma wani mutum daya da ba a tantance ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, irin wannan bayanin na jami’an tsaro ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kai wa al’ummar Cibiya da Karamai da ke Kufana, karamar hukumar Kajuru, inda aka kashe mutane biyu, wato Mista Idon Bonos da Mista Aston Namaskar yayin da wasu da dama suka jikkata.
Aruwan ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kashe mutane biyu a Damari, karamar hukumar Birnin Gwari, wato Salisu Mai Tireda da Mohammed Maikaba.
“Abin bakin ciki, gwamnatin Jihar Kaduna ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan da ‘yan bindiga suka kashe a hare-haren da suka kai a kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Kajuru,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa Gwamna Nasir El-Rufai, ya nuna matukar bakin cikinsa kan faruwar lamarin tare da mika sakon jaje ga iyalan wadanda aka kashe, yayin da ya yi addu’ar Allah ya jikansu da rahama tare da addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.