Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce rahoton sace matafiya a kan titin Abuja zuwa Kaduna ba gaskiya ba ne.
Wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar, ta ce gwamnatin jihar ta nuna rashin jin dadinta game da labarin wanda ta ce abin takaici ne.
- Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Shugabar Hukumar EU
- Za A Yi Mukabala Da Sheikh Idris A Bauchi Kan Kalamansa Game Da Manzon Allah SAWÂ
A ta ce labarin na karya ne, kuma tana aiki da jami’an tsaro don ganin ta gurfanar da wadanda suka asassa labarin ganin yadda ake samun ci gaba a jihar.
Aruwan, ya tabbatar da cewa rahotannin da suka samu daga jami’an tsaro da karamar hukumar Kagarko sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar kauyen Gwaje a Kagarko zuwa Jere a ranar Laraba, 5 ga Afrilu, 2023, inda suka yi garkuwa da wasu mutane biyu.
“Daga bayanan da ake da su, lamarin bai faru ba kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito. Bayanan da ke yawo cewar an sace matafiya ba gaskiya ba ne,” in ji Kwamishinan.
Aruwan ya ce gwamnatin Jihar Kaduna na bin diddigin jami’an tsaro kan duk wani abu da ya shafi tsaro da lafiyar ‘yan kasa.