Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ta nemi masarautar Saudiyya da ta zuba hannun jarinta a jihar Kaduna.
Dakta Sabuwa, ta yi wannan rokon ne a wajen wani taron da aka shirya domin murnar zagayowar ranar kasa ta masarautar Saudiyya karo na 93 a wajen taro ‘Efficent’ da ke jihar Kano.
- Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Sabbin Shirye-shiryen Inganta Tsaro A Jihar Kaduna
- Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bada Tabbacin Inganta Daidaiton Jinsi Da Karfafa Mata.
Mataimakiyar gwamnan ta godewa Masarautar Saudiyya bisa kyakkyawar niyyarta na ci gaba da tallafawa Nijeriya da jihar Kano da kuma Kaduna ta wata irin hanya.
Dakta Balarabe ta kara da cewa, jihar Kaduna kofofinta a bude suke domin zuba jari, ta kuma yi kira ga masarautar da ta karaso zuwa jihar Kaduna musamman ta fannin zuba jari.
Taron ya samu halartar babban jakadan masarautar Saudiyya, mai girma Khalil Ahmed Alwami, gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda ya kasance babban bako a taron. Gwamnonin jihohin Kaduna, Jigawa, Gombe da Zamfara duk sun samu wakilcin mataimakansu.
Sauran manyan bakin sun hada da wakilan Sarkin Kano da Sarkin Musulmi da jami’an gwamnati da shugabannin masana’antu da jami’an tsaro da sauran manyan mutane.