Gwamnatin Jihar Kaduna ta zargi tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, da kokarin jefa jihar cikin rashin kwanciyar hankali ta hanyar abin da ta bayyana a matsayin ayyuka masu tayar da hankali da ikirarin karya.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a Kaduna, kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dr. Suleiman Shuaibu, ya zargi El-Rufai da shirin dawo da jihar cikin rarrabuwar kawuna ta tashin hankali, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci kowanne yunkurin barazana ga zaman lafiya ba.
- Spence Na Dab Da Kafa Tarihin Zama Musulmi Na Farko Da Zai Buga Wa Ingila Ƙwallo
- An Kaddamar Da Cibiyar Raya Ilimin Dijital Ta Sin Da Afirka A Tanzania
“Gwamnatin ba za ta zauna ta yi shiru ta bar tsohon shugaba da ya bar jihar cikin halin tabarbarewa, ya tayar da rikici ya jefa Kaduna cikin wani sabon yanayi na tashin hankali na kabilanci da addini, rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki ba,” in ji wani bangare na sanarwar.
Dr. Shuaibu ya ce maganganun El-Rufai na baya-bayan nan, ciki har da zargin da ya yi a talabijin na kasa cewa gwamnati ta tarayya da ta jihar na “ba wa ‘yan ta’adda cin hanci,” karya ne, mai hadari, kuma an yi su ne don raunana kokarin tsaro. Ya kara da cewa Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaron (ONSA) ya riga ya musanta wannan zargi a matsayin mara tushe.
Ya ce hukumomin tsaro da shirye-shiryen cikin gida sun samu nasarori masu yawa a karkashin gwamna Uba Sani, inda ya bayar da misalin cafke manyan shugabannin ‘yan ta’adda da kuma dawo da kwanciyar hankali a yankunan da ke cikin tashin hankali kamar Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da Kachia.
Kwamishinan ya kara da zargin cewa El-Rufai ya kara kokarin yin tasiri bayan kalubalen siyasa da abokan siyasa na suka fuskanta a yayin zaben cike gurbi na 16 ga Agusta. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Gwamna Sani ta mai da hankali kan gina zaman lafiya, hadin kai da ci gaba, kuma ba za ta bar kowanne mutum ya “kawo koma-baya ga ci gaban da aka samu” ba. A daya bangaren kuma Kungiyar Kwararrun ‘Yan APC (ALP) ta nuna rashin jin dadi kan maganganun da ake danganta wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, inda ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kara wa ‘yan ta’adda karfi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp