Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta dauki karin ma’aikatan lafiya 9,000 cikin shekaru biyar masu zuwa.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ahmed Maiyaki, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Kaduna a wani taron kwana daya don tattaunawa da Kafafen Yada Labarai.
- Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno
- An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Hukumar Inshorar Lafiya ta Kaduna, KADCHMA ce ta shirya taron, tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta ta kiwon lafiya mai suna ‘Lafiya: UK-Nigeria Partnership for a Healthier Future’.
Maiyaki ya ce, “Gwamna Uba Sani kwanan nan ya ba da izinin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a karkashin rukunoni daban-daban.
“Za a ci gaba da yin hakan a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin inganta harkar lafiya a jihar.”
Maiyaki ya ci gaba da cewa, Gwamna Sani ya fifita harkar kiwon lafiya a gwamnatinsa, inda take gaba-gaba.














