Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta gina gidaje 10,000, musamman ga marasa karfi da ke yankunan karkara da birane a fadin kananan hukumomin jihar 23 nan da shekaru hudu masu zuwa.
Babban sakatare a ma’aikatar gidaje da raya birane ta jihar, Rabi’u Yunusa ne ya bayyana haka ranar Litinin a taron majalisar kasa da gidaje da raya birane karo na 12 da ya gudana a dakin taro na Umaru Musa Yar’adua, da ke filin taro na Murtala Square a Kaduna.
- Nijeriya Na Fuskantar Kalubale – Shettima
- Gwamnati Na Shirin Janye ‘Yansanda Masu Ba Da Tsaro Ga Hamshaƙai
Babban Sakataren ya bayyana cewa, Gwamnatin Kaduna a karkashin jagorancin Sanata Uba Sani a shirinta na sabunta birane, za ta gina gidajen ne ga masu kananan karfi a jihar Kaduna.
Yunusa ya bayyana cewa, aikin gina gidaje da gwamnatin jihar ta tsara yi, zai samar da gidaje masu saukin kudi a kananan hukumomi 23 na jihar.
A cewarsa, tuni Gwamna Uba Sani ya farauto wata kungiyar agaji ta kasar Qatar da za ta samar da gidaje 500 ga marasa galihu a jihar.
“Baya samar da gidaje 500 na agaji a karkashin gidauniyar Qatari Charity, gwamnatin jiha na da niyyar samar da karin gidaje 10,000 a cikin shekaru hudu masu zuwa.” inji Sakataren.