Yayin da ma’aikata a fadin Nijeriya ke yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Talata, Kamfanin Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), ya musanta rahoton da wata jarida ta yanar gizo ta fitar, inda tace, kamfanin wuta ya tsayar da raba wutar lantarki a fadin kasar sakamakon yajin aikin da ma’aikatan ke gudanarwa.
TCN, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun majalisar gudanarwarta, wacce LEADERSHIP ta samu kwafinta, ta ce, tashar wutar lantarki ta kasar nan tana nan cikin aminci, kuma tana samar da wutar lantarki mai yawa ga cibiyoyin rarraba wutar a fadin kasar.
- Ba Don Kishin Kasa ‘Yan Kwadago Suka Tsunduma Yajin Aiki Ba – Gwamnati
- Gwamnati Na Shirin Janye ‘Yansanda Masu Ba Da Tsaro Ga Hamshaƙai
“Kamfanin wutar lantarki na Nijeriya, TCN ya bayyana cewa, jaridar Daily Post ta buga wani labari, inda ta yi zargin cewa, shugaban hulda da jama’a na TCN ya ce, kamfanin zai tsayar da bada wuta, hakan ba gaske ba ne zallar karya ce da yaudara.
“Maganar bata da tushe balle makama domin TCN ta bakin Shugaban Hulda da Jama’a na kamfanin bai yi irin wannan kalamai ba.” Inji TCN
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp