Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin arewa maso yamma, Salihu Lukman ya bayyana cewa ko da ba a samu nasarar cire shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abudullahi Ganduje daga mukaminsa, an yi masa babban illa a siyasar a jiharsa.
Ya kara da cewa dalilin da ya sa gwamnatin Kano da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka yi nasarar illata siyasar Ganduje shi ne, lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar ya bar jihar tare da amintattun abokansa.
Lukman ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja mai taken “Hatsarin mummunan shugabancin APC.”
- Hisbah Ta Ware Wa ‘Yan Jarida Gurbin Mutane 50 A Auren Gata A Kano
- An Gurfanar Da Mutane 2 A Kotun Sojoji Kan Harin Tudun Biri
An dai kusan shafe wata guda ana yunkurin tsige Ganduje daga mukaminsa. A ranar Alhamis da ta gabata ce, masu zanga-zanga suka mamaye sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, domin neman Ganduje ya sauka daga kan mukaminsa jna shugabancin jam’iyyar, sannan a dawo wa yankin arewa ta tsakiya da mukamin wanda Abudullahi Adamu dan yankin ya rike kafin a bai wa Ganduje.
Masu zanga-zanga sun danganta bukatar ne kan dakatarwar da shugabannin mazaba Ganduje suka yi masa kan zargin amsar cin hanci da rashawa da gwamnatin Jihar Kano take yi masa.
Sai dai Lukman ya dage da cewa wannan lamari ba zai faru ba idan da a ce tsohon gwamnan bai dauke amintattun abokansa ba lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar APC suka bar Jihar Kano.
Ya ce, “A lokacin da Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa, dukkan shugabannin APC na Jihar Kano suka dawo Abuja. Wannan yana daga cikin dalilin da ya sa gwamnatin Jihar Kano ta samu nasarar illata siyasar Ganduje, saboda rashin shuganannin APC a Kano.
“Gaskiyar magana ita ce, tun lokacin da Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa tsawon wata tara sau biyu ya je Kano. Jam’iyyar adawa ce ke mulki a jihar kuma yana so APC ta kara kwace Kano.
“Idan har Shugaban kasa, Asiwaju Tinubu wanda yake da ayyuka da yawa zai je Jihar Legas fiye da sau biyar, tabbas abun kunya ne a ce Ganduje ya bayar da uzuri na kasa amfani da mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa wajen tallata siyasarsa. Raunin siyasa ne ake ya samu nakasu a mahaifarsa,” in ji shi.
Haka kuma dan siyasar na Jihar Kaduna ya zargi Shugaba Tinubu kan ci gaba da mayar da yankin arewa ta tsakiya saniyar ware daga mukamin shugabancinsa.