Gwamnatin Kano ta fitar da gargadi na karshe ga ma’aikatan gwamnati wadanda suka gaza kammala tsarin tantancewar da ake yi, inda ta ce duk wanda ya gaza cika wannan umarnin zai fuskanci matsala daga aikinsa.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai. Ya jadadda cewa ba za a biya duk wanda bai cika tsarin tantancewar ba, wanda yake gudana kusan shekara guda.
- Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu
- Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024
“Ya zama wajibi a garemu mu magance wannan matsala sakamakon rahoto kin biyan albashi da sakaci da aiki. Gwamnati na kara jajircewa wajen tabbatar da walwalar ma’aikata, sannan kuma gwamna ya ba da umarnin gudanar da kyakkyawan bincike kan lamarin,” in ji shi.
Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoton da kwamitin da gwamnati ta kafa kan batun matsalar da aka fuskantar ta albashin ma’aikata. Yayin da ake ci gaba da nazarin rahoton, gwamnatin tan gabatar da wasu matakin gaggawa domin kare faruwar haka nan gaba.
Haka zalika, sakataren gwamnatin ya sanar da cewa gwamnati za ta gabatar da sabon jadawalin biyan albashin (Payroll) ta hanyar bugawa tare da raba bayanan albashin ga dukkan ma’aikatu, hukumomin gwamnati da kananan hukumomi domin dubawa.
A cewarsa, domin tabbatar da gudanar da wannan tantancewar, an samar da kwakkwaran kwamitoci a matakin jiha da kananan hukumomi tare da sauran sassan hukumomin da ke da alaka da kudi, sannan an ba su umarni samar da dukkan bayanan biyan albashin nan take.
Farouk ya bukaci ma’aikatan da matsala ta shafa su kai kansu gaban hukumominsu tare da nagartattun bayansu kan dalilin kin bin wannan umarni, saboda a kula da sabunta kundin biyan albashin.
Ya ce Mambobin kwamitin sun hada da manyan sakatarorin daga manyan ma’aikatu, wakilai daga kwamitin tsara jadawalin albashi da kuma wasu manyan jami’an a ofishin sakataren gwamnatin Jihar Kano. Sannan ya jadadda cewa bin wannan umarni ya zama wajibi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp