Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, ta ƙara wa’adin dakatar da nuna wasu fina-finai 22 da aka dakatar da su.
Tun da farko, hukumar ta dakatar da fina-finan ne saboda sun rashin tangance su.
Ta kuma bai wa masu fina-finan mako ɗaya su gyara kurakurensu.
Sai dai yanzu, bayan wani zama da aka yi tsakanin hukumar da wakilan masana’antar Kannywood, an amince a ƙara mako guda domin bai wa masu fina-finan damar gyara fina-finansu, saboda ka da su yi asara.
Shugaban ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN) reshen Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, ya ce an samu daidaito bayan ganawa da shugaban hukumar tace fina-finai, Abba Al-Mustapha da wasu jami’ansa.
An shirya sake zama a ranar Alhamis mai zuwa don kammala tattaunawar gaba ɗaya.
Cikin waɗanda suka halarci ganawar har da wakilan MOPPAN kamar su Abdul Amart, Nazifi Asnanic, da Abubakar Bashir Maishadda.