Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan ₦2,910,682,780 don biyawa ɗalibai 119,903 kuɗin jarrabawar NECO da NBAIS ta shekara 2024.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai a Kano, inda yace duk wani ɗalibi da ya samu darussa hudu daga cikin darussan da ya rubuta Jarrabawar samun cancatar zana Jarrabawa a jihar zai amfana da shirin biyan kudin jarabawar na gwamnatin Kano, sannan za a yi masa rijistar zama don zana Jarrabawar.
Doguwa ya kara da cewa, Gwamnati za ta biyawa kowane ɗalibi ₦24,250 da kuma dubu ₦21,000 don zana Jarrabawar NECO da NBAIS, tare da bayanin cewa Gwamna ya yi fatali da shawara biyawa kowane ɗalibai kuɗin jarrabawar sai wanda ya lashe darussa hudu a kowane darasi.
Ya bukaci iyaye da ka da su dakatar da yaransu zuwa makaranta saboda sun fadi jarrabawar neman cancanta, inda ya nuna cewa gwamnati ta jajirce wajen inganta sashin ilimi, musamman aniyarta na sanya dokar ta ɓaci a sashin ilimi,
Doguwa ya gargaɗi shugabannin makarantun Sakandire da sauran malamai kan sauya sunan ɗalibi da su kiyaye, inda ya ce duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifi zai dandana kudarsa.