Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen siyan duk wani fili da ke kewayen Jami’ar Bayero ta Kano, saboda yadda ayyukan masu satar filaye ke karuwa a kadarorin jami’ar da ke unguwar Rimin-Zakara a jihar.
Da yake gargadin a ranar Juma’a, Baffa Baba Dan-Agundi, shugaban kwamitin yaki da gine-ginen, ya ce abin takaici ne yadda wasu mutane suka mamaye filayen gwamnatin tarayya suna sayar wa jama’a da ba su ji ba gani ba.
- Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa Sojojin Da Suka Kashe ‘Yan Bindiga 152 Tare Da Lalata Sansani 100
- ‘Gaskiyar Lamari Game Da Zargin Amfani Da Sinadarin Mercury A Rigakafin Yara’
Ya ce gwamnatin jihar ta lura da yadda masu sa ido kan filaye ke kwace wani bangare na kadarorin da karfi da yaji a yankin.
“Na yi kira ga jama’a da su guji yin cinikin filaye ba bisa ka’ida ba a filin jami’ar ta hannun dillalan filaye da ba a amince da su ba, duk wanda ya yi haka to zai fuskanci hukunci.
“Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ruguza duk wani gini na haram ko wani tsari da aka tada a kadarorin jami’ar ba,” a cewarsa.
DanAgundi ya ce gwamnatin jihar ta gana da hukumomin tsaro da shugabannin jami’o’in, inda suka tabbatar da cewa al’ummar Rimin-Zakara ba su da hannu a wannan haramtacciyar sana’a, don haka gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai gaggauta duba lamarin tare da kamo duk masu hannu a ciki don yi musu hukunci.