Gwamnatin Jihar Kano kaddamar da dokar ta-baci game da kwacen waya da kuma wasu laifukan da ake aikatawa a birnin.
Majalisar dokokin jihar ta nuna damuwa kan matsalolin kwacen waya da sane da shan miyagun kwayoyi da ma wadansu laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.
- Ba Zan Je Saudiyya Ba Ina Nan Daram A Turai — Lukaku
- Abba Ya Aike Wa Majalisar Dokokin Kano Sunan Mutum 19 Da Zai Nada Kwamishinoni
A wata mahawara da shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar, ‘yan majalisar sun amince kan cewa akwai bukatar a gaggauta magance matsalar kafin ta yi kamari.
Majalisar dokokin ta kuma amince da wani kudurin da ya bukaci gwamnatin jihar ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin hukunta wadanda aka kama da laifi.
Kwacen waya dai ya zama ruwan dare a Kano, lamarin da ya sanya wasu rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata.