Gwamnatin Jihar Kano ta kai tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, tsohon Shugaban Hukumar Masu Jigilar Kayayyaki ta Nijeriya, Hassan Bello, da wasu mutane biyar kotu bisa zargin karkatar da Naira biliyan 4.49 da aka ware don aikin Dala Inland Dry Port.
An shigar da ƙarar a Babbar Kotun Jihar Kano, inda ake zarginsu da haɗa baki, almundahana, da cin amana.
- Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
- 2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara
Waɗanda ake tuhuma sun haɗa da ‘ya’yan Ganduje biyu da wasu tsofaffin hadimansa.
A cewar ƙarar, ana zargin cewa sun canja kashi 80 cikin 100 na hannun jarin kamfanin, ciki har da kashi 20 na gwamnatin jiha, zuwa wani kamfani na bogi mai suna City Green Enterprise, sannan suka karkatar da kuɗin aikin zuwa aljihunsu.
Sai dai kamfanin Dala Inland Dry Port ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa babu wani daga cikin iyalan Ganduje da ke da hannun jari ko muƙami a kamfanin.
An tsara fara sauraron ƙarar a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025, a gaban Mai Shari’a Yusuf Ubale.














