Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jaddada aniyarsa na karfafa hadin gwiwar da gwamnatin jihar ta yi da gidauniyar Bill & Melinda Gates shekaru 11 da suka gabata.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya bayyana bukatar samar da alluran rigakafi kusan miliyan shida domin yaki da cutar diphtheria a jihar.
- Emefiele Bai Bayyana A Gaban Kotu Ba Yau
- Sake Bude Sansanin NYSC Na Borno Ya Tabbatar Da Zaman Lafiya Ya Samu A Jihar – Zulum
A yayin wani taro da aka yi a gidan gwamnati da ke Kano a ranar Talata, Gwamna Yusuf ya tabbatar wa da wakilan gidauniyar kudurinsa na hadin gwiwa da ake da su na inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamaref Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana haka a lokacin da yake karbar tawagar gidauniyar a madadin Gwamnan jihar, inda ya jaddada aniyar jihar na inganta harkar lafiya a dukkan matakai.
A cewar wata sanarwa da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Garba Shuaibu ya aikewa manema labarai a ranar Laraba, ya ce gwamna Yusuf ya bayyana bukatar samar da alluran rigakafi kusan miliyan shida domin yakar cutar a jihar.
“Ya kuma nuna godiyarsa ga gidauniyar bisa tallafin da ta ke bayarwa a fannin kiwon lafiya tare da nuna sha’awarta ga yadda gidauniyar ke shiga harkar noma,” in ji shi.
Mista Jerremy Zungurana, shugaban tawagar gidauniyar ta Nijeriya, ya yaba da hadin gwiwar da aka samu, sannan ya yaba da kokarin jihar a fannin kiwon lafiya.
Ya kuma yi alkawarin bayar da tallafi mai dorewa ga ayyukan jihar kamar yadda Gwamna Yusuf ya bukata.