Gwamnatin Jihar Kano ta shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar kiwon lafiya, domin ba su damar samun ingantaccen kiwon lafiya kyauta yayin da suke tsare.
Sanarwar ta fito daga Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Kano, CSC Musbahu Kofar-Nasarawa, a ranar Litinin.
- Ɓarayin Wutar Sola Sun Baƙunci Lahira Yayin Da Suke Tsaka Da Kwancewa
- Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Farko Kan Bincike Da Aikace-Aikacen Tashar Sararin Samaniya
Babbar Sakatariya a Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Kano, Dokts Rahila Aliyu-Mukhtar, ta bayyana hakan yayin wata ziyara da ta kai ga Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Kano, Kwanturola Ado Salisu.
Ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da wannan shiri, wanda zai taimaka wajen tabbatar da cewa fursunoni suna cin gajiyar ingantaccen kiwon lafiya yayin da suke tsare.
“Walwalar fursunoni ta fuskar kiwon lafiya yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da kyakkyawan tsarin gyaran hali da kuma dawo dasu cikin al’umma da cikakken lafiya,” in ji Rahila.
Wannan matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na inganta rayuwar dukkanin jama’ar jihar, ciki har da fursunonin da ke gidajen gyaran hali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp