Gwamnatin jihar Kano za ta karbi bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar.
Tun da farko gwamnatin jihar ta dage ziyarar zuwan shugaba Buhari da ta shirya yi, inda ta ce ta yi hakan ne domin kauce wa fushin jama’arta sabida kin dage wa’adin dawo da tsoffin kudaden naira asusun bankuna da gwamnatin Buhari ta yi.
Bayan da gwamnati ta sanar da tsawaita wa’adin, gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ce jihar Kano ta shirya tsaf domin tarbar shugaban kasar.
Ganduje tare da Barau Jibrin – shugaban kwamitin majalisar dattawa kan tsare-tsare, ya jagoranci tawagar jihar inda suka gana da shugaba Buhari a Daura, anan ne aka sanar da cewa, ziyarar shugaba Buhari zuwa Kano za ta tabbata kamar yadda aka tsara tun farko.