Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), ta tabbatar da ɓullar cutar Mpox a jihar.
Hukumar ta ce marasa lafiyar da suka kamu da cutar sun warke gaba ɗaya kuma an sallame su.
- He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
- Jadawalin ‘Yan Wasa 30 Na Farko A Kyautar Ballon D’or Ta Bana
Daraktan KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu Abbas ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce mutum biyun sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Birni da Ungogo.
Ya ƙara da cewa duk mutanen da suka yi hulɗa da marasa lafiyar an yi musu gwaji, kuma babu wanda aka samu da cutar.
Farfesa Abbas ya bayyana cewa wannan tabbaci ya biyo bayan gargaɗin da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta yi, na kiran jihohi da su ƙara sa ido kan ɓarkewar cututtuka kamar COVID-19, Ebola, Zazzaɓin Lassa, Marburg da Mpox.
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.
KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.
Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.
Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.
Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp