Gwamnatin Jihar Kano ta yi barazanar ɗaukar matakin hukunta matasa da ke haddasa rikice-rikice a wasu unguwanni na jihar, tare da gargaɗinsu da su daina duk wani aiki da zai sanadi wajen taɓarɓarewar zaman lafiya.
Wannan gargadi ya fito ne daga Kwamishinan tsaro da harkokin musamman, Air Vice Marshal Ibrahim Umar (rtd), yayin wata ziyara da ya kai Kurna Tudun Fulani, ƙaramar hukumar Dala, inda aka fi samun tashin hankali.
- Jami’ar FUDMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina
- ‘Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Wata Matar Aure, ‘Yar shekara 22 A Kano
Kwamishinan ya bayyana cewa rikicin da aka samu kwanan nan ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi mai suna Abba Sa’idu, inda ya jaddada ƙudurin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ɗaukar matakan samar da tsaro da kuma koyar da matasa sana’o’i domin basu damar dogaro da kai. Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnati na aiki kafaɗa da kafaɗaa da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a duk faɗin jihar.
Ya kara da cewa tsaro na buƙatar haɗin kai daga kowa da kowa, don haka ya bukaci kowane gida da ya taimaka wajen bayar da rahoton duk wani abu ko mutumin da ake zargi ga jami’an tsaro. Wannan mataki na da nufin rage yawaitar aikata laifuka da kuma kawo ƙarshen matsalolin tsaro a yankin.
A ɓangarensa, Mai Unguwar Kurna Tudun Fulani, Malam Usaini Ibrahim, ya roƙi gwamnati da ta gina ofishin ‘yansanda a cikin unguwar domin ƙarfafa tsaro, inda ya bayyana cewa al’umma za ta bayar da filin da ya dace domin gina ofishin. Wannan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp