Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta binciki musabbabin gobarar da ta tashi a sakatariyar mulki ta karamar hukumar Gwale.
Gobara ta tashi sakatariyar mulki ta karamar hukumar a ranar 13, ga watan Disambar 2023, inda ta shafi ofisoshi 18 tare da lalata dukiyoyin miliyoyin Naira.
- Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar NNPP Na Kara Rincabewa A Kano
- Gwamnatin Kano Za Ta Biya Wadanda Ta Yi Wa Rusau Diyyar N3bn
Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Gwarzo, ne ya bayyana hakan a wata ziyarar da ya kai sakatariyar karamar hukumar domin duba irin barnar da gobarar ta yi.
Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Kabiru Yusuf na aiki tukuru domin ganin an yi adalci a hukuncin kotun koli mai zuwa.
Gwarzo wanda shi ne kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, ya bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda.
Ya kuma tabbatar da cewa duk da tashin hankali da ake fama da shi a jihar saboda lokacin da ake jira na yanke hukunci, gwamnatin mai ci ta shagaltu da samar da ayyuka cigaba da za su daukaka rayuwar al’umma jihar..