Mataimakin gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano za ta yi bincike da kuma fassara litattafan kimiya da fasaha da harshen Hausa, dimun bunkasa ilimi da ci gaban al’ummar jihar.
Mataimakin gwamnan ya bayana haka a wajen bikin ranar kimiya da fasaha ta duniya, da ma’aikatar kimiyya da fasaha karkashin jagoranci kwamishinan kimiyya da fasaha na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tajo Usman, ta shirya a tun daga ranar Juma’a zuwa Litinin da ta gabata.
- Wasu Muhimman Abubuwa Da Ba A Sani Ba Game Da Kwakwalwa
- An Kaddamar Da Shirin Bidiyo Na CMG Mai Taken “Daga Great Wall zuwa Machu Picchu”
A cewar mataimakin gwamnan, yanzu haka gwamnatin Jihar Kano ta kafa gwamitin bincike da fassara litattafan kimiya da fasaha da Hausa ganin yadda wannan ilimi yake da muhinmanci da kuma yadda kasashen duniya suke koyar da ilimummuka da harshensu na asali, domun saukin fahimta da ganewa musammam ganin yadda daliban suke da kaifin basira.
Ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin Kano ta kudiri samar da cibiyoyin koyar da kwamfitoci a kananan hukumomi 44, domin kawar da matsalolin da dalibai suke fuskanta a lokacin jarabawa JAMB.
A nasa jawabin, kwamishinan kimiya da fasaha na Kano yaba wa gwamnatin Kano karkashin shugabancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa da daukacin jami’an gwamnatin Kano da al’umma kan irin goyan bayan da suke samu na gudanar da ayyuka a wannan ma’aikata da ke kokarin bunkasa ilimun kimiyya da fasaha a Kano.
Masanin kimiyya da fasaha, Farfesa Dahiru Sale ya nuna yadda wannan gwamnati ta ba ilimi muhinmancin da kuma yadda bangaren kimiyya da fasaha ya samu goyan bayan gwamna kan duk abun da ake bukata, wanda wannan ne ya sa makarantun kimiyya da fasaha kashi 75 cikin 100 suka lashe gasar da ma’aikatar kimiyya da fasaha ta shirya a tsakanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu a Kano.