Gwamnatin Jihar Kano, za ta kashe Naira biliyan 2.5 a auren gata a shekarar 2025.Â
Za a gudanar da bukukuwan auren cikin kowane wata uku a dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
- Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Sun Samu Karuwar Kudin Shiga A 2024
- Abin Da Ya Sa Masu Ruwa Da Tsaki Suka Gana Da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur
Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi na jihar, Musa Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin 2025, wanda ya ƙunshi Naira biliyan 91.32 don gudanar da mulki da kuma hidimar jama’a.
Ya ce gwamnati na ƙoƙarin inganta rayuwar al’umma da tabbatar da adalci a cikin al’umma.
Har ila yau, ya bayyana cewa kasafin kudin ya tanadi Naira biliyan É—aya don shirye-shiryen azumin watan Ramadan, Naira miliyan 955 don gudanar da harkar ilimi, da Naira biliyan 1.049 don siyan injinan buga takardu, gyaran tsarin samar da ruwa, da kuma kayan aiki a É—akunan karatu.
Bugu da ƙari, Naira miliyan 267.6 an ware su domin shirye-shiryen Addinin Musulunci da tallafa wa waɗanda suka Musulunta, yayin da Naira miliyan 589 za a yi amfani da su wajen bincike kan harkokin tsaro da kuma yaƙi da bara a tituna.
Jimillar kasafin kuÉ—in Jihar Kano na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 719.75, wanda ya karu da kashi 31 daga asalin kuÉ—in da aka gabatar da farko, kuma ya fi na shekarar 2024 da kashi 65.