Gwamnatin Jihar Kano ta cika alƙawarin da ta ɗauka ga al’ummar ƙauyen Gadan, ƙaramar hukumar Gezawa, inda aka kona masallata a lokacin Sallar Asuba.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Litinin, yana mai cewa gwamnati ta amince da kashe Naira miliyan 151,863,895.97 domin gudanar da muhimman ayyukan ci gaba a garin.
- Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kona Masallata A Kano
- Yadda Rikici Ya Yi Sanadin Kashe DPO A Kano
Ayyukan sun haɗa da gyara da faɗaɗan masallacin da aka ƙona masallatan a ciki, da ginin sabuwar makarantar Islamiyya da ofishin malamai, da gyaran banɗakuna guda shida, da kuma aikin famfon tuka-tuka mai amfani da hasken rana tare da ƙarin tanki a sama.
Al’ummar ƙauyen Gadan sun bayyana matuƙar farin cikinsu da wannan ci gaba, inda suka bayyana cewa irin wannan cika alƙawarin na nuna shugabanci nagari da kishin jama’a.














