Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta samar da ƙarin dakarun tsaro na C Watch 200, domin murƙushe ɓarayin daji da suka addabi wasu yankuna na jihar.
Wannan dai shi ne karo na uku da gwamnatin Jihar Katsina ta horas da dakarun tsaro, sannan ta ƙaddamar da su domin tura su wuraren da ake fama da matsanancin rashin tsaro a jihar.
Da yake jawabi a taron yaye sabbin dabarun tsaron da ake yi wa laƙabi da dakarun Dikko, Gwamnan Raɗɗa ya bayyana cewa Jihar Katsina ta hau hanyar samun zaman lafiya mai ɗorewa.
- Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina
- Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina
“Lokacin da muka ƙaddamar da dakarun tsaro shekaru biyu da suka gabata, mun yi haka ne da niyar fatatakar ɓarayin daji, sai dai wannan gwamnati tamu tana fuskantar ƙalubale na rashin tsaro a wasu ɓangarori na jihar, ” in ji shi.
A cewarsa, waɗannan sabbin dabarun tsaron da aka ƙaddamar za a tura su ne a ƙananan hukumomin Kankiya da Dutsima, wanɗada take da iyaka da Safana da Ɗanmusa da kuma Matazu da ‘yan bindigar ke yawan kai hare-haren wuce gona da iri.
Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa wannan zaman sulhu da ɓarayin daji da ake yi al’umma ce take yi ba wai gwamnati ba, ita gwamnati tana iya yin sulhu da ɗan bindigar da ya tuba ya yarda da zaman lafiya kuma ya ajiye mukaminsa.
A cewarsa, rawar da gwamnati take iya takawa shi ne, ta ƙarfafa zaman lafiya, sannan ta tabbatar an bi doka da oda a cikin al’umma. Ya ce abubuwa da gwamnati ke lura da su shi ne, al’umma ta mori zaman lafiya domin bunƙasar tattalin arziki da sauran su.
Tunda farko a jawabinsa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Hon. Nasiru Mu’azu Danmusa ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya rage ƙarfin harkokin rashin tsaro a Jihar Katsina.
Haka kuma ya bayyana cewa wannan ne karo na uku da aka ƙaddamar da bikin yaye dakarun tsaro na Malam Dikko Raɗɗa, sannan za a sake ƙaddamar da sauran a watan Nuwambar wannan shekarar idan Allah ya kai mu rai da lafiya.












