Gwamnatin Jihar Katsina ta gano ma’aikata 3,488 na bogi bayan gudanar da tantancewar yatsun ma’aikata a ƙananan hukumomi 34 da hukumomin ilimi na jihar.
Daga cikin ma’aikata 50,172 da aka tantance, an tabbatar da 46,380 kawai.
- Labaran Xinjiang a Zane: Yadda Hamada Ta Zama Gonaki
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Kakkaɓe Masu Amfani da Takardun Bogi a Ma’aikatunta
Sauran kuma an cire su saboda laifuka kamar amfani da takardun bogi, yin ƙarya kan shekarun haihuwa, ƙin zuwa aiki, ƙarin girma ba bisa ƙa’ida ba.
Kwamitin ya kuma karɓo Naira miliyan 4.6 daga ma’aikatan da ke karɓar albashi daga gwamnatoci biyu (jiha da tarayya).
Haka kuma an gano ma’aikata guda shida da suka ci gaba da karɓar albashi duk da suna hutun aiki.
A wani labarin kuma, Sakataren Ilimi na ƙananan hukumomi, ya gabatar da ma’aikata 24 na bogi domin tantancewa, abin da ya nuna girman almundahanar da ake yi a ɓangare ilimi.
Gwamna Umaru Dikko Radda ya umarci a hanzarta fitar da takardar da su domin aiwatar da shawarwarin kwamitin.
Ya ce gyare-gyaren za su taimaka wajen mayar da kuɗaɗe ga ci gaban ƙananan hukumomi tare da kare jihar daga almundahana.
Yanzu haka, ƙananan hukumomi sun ajiye Naira miliyan 500, kuma ana sa ran adadin zai kai Naira biliyan 5.7 idan aka dakatar da biyan ma’aikatan bogi.
Gwamnan ya jaddada cewa duk da gargaɗin cewa irin wannan gyara na iya cutar da siyasarsa, jihar ta fi buƙatar gaskiya da tsari wajen kashe kuɗaɗe domin inganta shugabanci da ƙara amincewar jama’a.