A kokarin da ake yi na daukar matakin magance rikice-rikicen da ke tsakanin makiyaya da manoma, gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da kwamiti na wucin gadi wanda zai rinka kula da duk wani kai-kawo na makiyaya a fadin jihar.
Sakataren gwamnati Barista Abdullahi Garba Faskari ya kaddamar da nadin a madadin gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda.
- Masana’antar Kannywood Ta Sauka Daga Kan Turbar Da Tun Farko Aka Ginata -Tahir Fagge
- Matsalar Tsaro: Matawalle Ya Ziyarci Jihar Zamfara
Ya bayyana cewa, a wannan lokacin na girbi akwai yiwuwar samun damuwa kan rikice-rikice a tsakanin manoma da makiyaya, a inda makiyaya ke sakin dabbobinsu ba da gangan ba kan gonakin manoma wanda hakan kan haddasa rikici.
Sakataren gwamnati ya jaddada cewa kwamitin ya samar da jituwa da kuma magance hadarurruka. Kwamitin ya samu halartar babban sakatare, Salisu Abdu da wakilai da kuma jami’an tsaro.
Kwamitin ya samu wakilai daga sassa daban-daban wanda suka hada da kungiyar miyatti Allah kautar hore, ma’aikatar tsaro ta cikin gida, ma’aikatar harkokin addini da kuma ma’aikatar aikin gona.
Kudirin na Gwamna Radda na da nufin jajircewa wurin kawo tsaro da samar da zaman lafiya a yankunan da kuma tabbatar da cewa manoma da makiyaya sun zauna lafiya ba tare da rikici ba a lokacin girbi.