Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da shirin bude shagunan sayar da kayan masarufi a farashi mai rahusa guda 38, wadanda aka yi wa lakabi da ‘Rumbin Sauki’ a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.Â
An bayyana hakan ne bayan zaman majalisar zartarwa na jihar karo na 10, wanda ke da nufin samar da kayayyakin amfanin yau da kullum a farashi mai rahusa don rage tsadar rayuwa.
- Ban Yi Nadamar Yakar PDP A Zaben 2023 Ba – Wike
- Ba Mu Da Hannu A Kara Farashin Man Fetur – Gwamnatin Tarayya
Mai bai wa gwamnan shawara kan Tattalin Arzikin Karkara, Injiniya Yakubu Nuhu Danja, ya bayyana cewa babban birnin jihar zai samu karin shaguna guda biyu, yayin da Daura da Funtua za su samu guda daya kowane saboda yawan al’ummar yankunan.
Wadannan shagunan za su kasance wani bangare na shirye-shiryen Gwamna Radda na rage wa jama’ar jihar radadin tsadar rayuwa, musamman a wannan lokaci da kalubalen tattalin arziki ke kara tabarbarewa.
Gwamnan ya tabbatar da aniyarsa ta na samar da wannan shiri a Jihar Katsina, bayan ya kaddamar da ire-iren wadannan shaguna a Jihar Jigawa yayin wata ziyara.
Gwamna Radda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar wa jama’a sauki ta hanyar saukaka samu wajen kawo kayayyaki masu rahusa.
Ya kara da cewa, gwamnatinsa tana son inganta rayuwar al’ummar Jihar Katsina ta hanyar rage nauyin da ke kan magidanta, wanda ta haka ne za a samu ci gaba mai dorewa wajen magance matsalolin tattalin arziki da al’ummar jihar ke fuskanta.