Gwamnatin Jihar Kebbi ta ba da ƙwangilar shimfiɗa hanyoyi guda huɗu a yankin Barikin Mopol da ke Badariya, Birnin Kebbi, kan kuɗin Naira biliyan 2.174 ga kamfanin B-TECH Global Services Ltd. An sanya hannu kan yarjejeniyar kwangilar a ofishin Kwamishinan Ayyuka na jihar, Hon. Abdullahi Umar Faruk Muslim.
Kwamishinan ya bayyana cewa aikin zai haɗa da shimfiɗa tituna da kuma magudanan ruwa domin gujewa ambaliyar ruwa. Ya ce wannan wani ɓangare ne na shirin Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu wajen samar da ci gaba ga al’ummar jihar, musamman mazauna unguwar Badariya wadda ke da yawan jama’a.
- ‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi
A cewarsa, za a gudanar da aikin cikin watanni 18 tare da sanya ido daga injiniyoyin gwamnati domin tabbatar da inganci. Haka kuma ya gargaɗi kamfanin da kada ya kuskura ya yi aiki maras kyau, yana mai jaddada cewa gwamnati ta tanadi ƙa’ida wacce ke wajabta kamfani ya kula da aikin tsawon shekara guda kafin a miƙa shi ga gwamnati.
An bayyana cewa za a biya kamfanin kashi 40% na kuɗin kwangilar a matsayin kuɗin farko domin fara aiki. Wakilin kamfanin, Bashar Shamaki, ya tabbatar da cewa za su fara kawo kayan aiki cikin sati biyu tare da gudanar da aiki mai inganci, yana mai gode wa gwamnatin jihar bisa wannan amincewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp