Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya tabbatar wa sarakunan gargajiya cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da sanya su cikin tsare-tsaren gudanar da mulki da kuma shirye -shiryen ci gaba don inganta rayuwar al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar al’ummar garin Besse ta kai masa ziyarar godiya a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi, domin nuna jin dadin nadin Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin sabon Uban kasar Besse (Barade na biyu) da ke karamar hukumar Koko-Besse.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Kasuwar Dodoru A Jihar Kebbi, Rumfuna Da Yawa Sun Lalace
- Zanga-zanga: Daga Tutar Rasha Cin Amanar Kasa Ne – Janar Musa
Gwamna Nasir ya jaddada kudirin gwamnatinsa na shigar da Sarakunan cikin shirye-shiryen raya jihar da kasa baki daya, inda ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta amince da aikin gyaran hanyar Koko-Besse zuwa Zariya-Kalakala zuwa Bagudo, kuma nan ba da jimawa ba, za a fara aikin hanyar.
Ya kuma bayyana shirin bunkasa garuruwan yankin da sauran sassan jihar bayan kammala aikin gyaran fuska na babban birnin jihar. Ya kara da cewa, gwamnati za ta gyara makarantu 30 zuwa 50 a Koko-Besse domin inganta ilimi a yankin.
Har ilayau, Gwamnan ya taya Farfesa Bande murnar nadin da aka yi masa, inda ya bayyana shi a matsayin fitaccen malami kuma jami’in diflomasiyya wanda ya yi hasashe tare da daukaka martabar jihar Kebbi da Nijeriya a fagen kasa da kasa. Ya kuma bai wa Farfesa Bande tabbacin goyon bayansa wajen tafiyar da mulkin al’ummarsa cikin nasara.
Tun da farko, a jawabinsu, Uban kasa, kuma Dutsinmari, Alhaji Muhammadu Mu’allah’yidi Usman da Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo a madadin al’ummar Besse sun gode wa Gwamna Nasir Idris bisa amincewa da nadin Farfesa Bande. Sun bayyana gamsuwarsu kan yadda Farfesa Bande zai iya yin amfani da kwarewarsa da iliminsa wajen bunkasa gundumar tare da yin kira ga gwamnan da ya ba sabon Uban kasar goyon baya.