Gwamnatin jihar Kogi ta bakin ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta gabatar da wata takarda da ke tuhumar sarki mai lambaya ta daya, Ohimeghe-Igu na Koton-Karfe Alh. Abdulrazak Isa-Koto, bisa zarginsa da hannu a siyasar bangaranci.
Tuhumar na kunshe ne a wata takarda mai kwanan wata 22 ga Nuwamba, 2023, mai dauke da sa hannun kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Bar. Salami Momodu Ozigi Deedeat.
- Za Mu Samar Da Wutar Lantarki MW60 Ko Sola MW50 A Kowace Jiha -Gwamnonin Arewa Maso-Gabas
- Sojoji Da ‘Yan banga Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi
Wasikar ta bawa sarkin kwanaki biyu kacal da ya kare kansa ta hanyar rubutu game da zargin da gwamnatin ke yi masa.
LEADDERSHIP ta tattaro cewa, tuhumar ba za ta rasa nasaba da yawan ziyarar da wasu ‘yan takara a zaben gwamnan jihar da aka kammala a jihar suka kai fadar sarkin gargajiyar ba. Lamarin da ya haifar da wani mummunan lamari inda wata mai goyon bayan APC ta rasa ranta a wani gangamin yakin neman zabe.