Gwamnatin Jihar Kogi ta yi Allah wadai da mummunan harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai da ya hallaka mutane da dama a jihar.
A ranar Lahadin nan da ta gabata ne dai wasu ‘yan bindiga su ka kai harin a yankin Ogananibo da ke cikin karamar hukumar Dakina ta jihar Kogi, inda su ka hallaka jama’a da dama tare da jikkata wasu da dama.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Kisan Basarake Da Garkuwa A Neja
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Kisan Basarake Da Garkuwa A Neja
Tuni dai gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa da ke yin Allah wadai da wannan hari na aika-aika.
Mista Kingsley Fanwo shine kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, ya ce gwamnati ta kadu sosai da samun wannan mummunan labari.
Ya ce gwamnatin Jihar Kogi ta yi Allah wadai da wannan hari kuma tana daukar duk wasu matakai da su ka wajaba na kare rayukka da kuma dukiyar jama’a, kana ya ce tuni gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ba da umarnin tura karin jami’an tsaro a yanki.
Da yake karin bayani akan adadin wadanda suka mutu a harin, kwamishinan yada labaran ya ce jami’an tsaro na kan bincike, ba su gama tantancewa ba.
A yanzu haka hukumar bayar agajin gaggawa ta Jihar Kogi ta isa yankin da lamarin ya faru domin ba da agaji ga wadanda su ka jikkata.
Suma dai wasu al’ummar Jihar Kogi sun yi Allah wadai da wannan hari a wannan wata na Ramadan da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar Azumi.
A nasa bangaren, Shugaban Kungiyara Izala a Jihar Kogi, Yahaya Dalladi Musa, ya ce a wannan watan mai alfarma na Ramadan wata ne na zaman lafiya da ibada ba wata ne na tashin hankali ba kuma duk wadanda suka yi wannan abu ba su kyauta ba.
Jihar Kogi dai na fuskantar karin hare-haren ‘yan bindiga dama masu yin garkuwa da mutane, al’amarin da ke matukar bukatar kulawa ta musamman domin shawo kan lamarin