Gwamnatin jihar Kogi ta yi barazanar hukunta duk wanda ya ki karbar tsofaffin takardun kudi a jihar.
A cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai da sadarawa na jihar Kingsley Fanwo ya fitar ya ce, kin karbar tsofaffin takardun kudin, tamkar kin yin biyaya da hukuncin da kotun koli ta yanke ne na cewa, a ci gaba da karbar kudin har zuwa ranar 31 ga watan disambar 2023.
Fanwo ya ci gaba da cewa, ba za ta samu yadda ‘yan kasuwa da kuma daidaikun mutane a jihar ke ci gaba da kin karbar tsofaffin takardun kudin ba.
Ya umarci ‘yan jihar da su kai rahoton duk wanda ya ki karbar tsofaffin takardun kudin ga jami’an tsaro da ke a jihar domin gwamnatin ta dauki matakin da ya dace.
Ya kima yi barazana ga bankunan kasuwanci a jihar da suka ki karbar tsofaffin takardun kudin, inda ya ce, gwamnatin jihar za ta iya garkame bankunan na su.
Kwamishin ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta kafa kwamti mai karfi da zai tabbatar da an kiyaya wannan gargadin da ta yi tare da yin amfani da hukuncin da kotun ta yake.