A yayin da gwamnatin jihar Legas ta fara aiwatar da dokar hana zirga-zirgar baburan kasuwanci da aka fi sani da Okada a ranar Laraba, hukumar kula da jiragen ruwa ta Legas (LAGFERRY) ta ce ta tura karin jiragen ruwa don kara tafiye-tafiyen aiki na yau da kullun a tashoshi da jiragen ruwa da ke yankunan da abin ya shafa.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa dokar hana gudanar da ayyukan Okada ta shafi kananan hukumomi shida da kuma kananan hukumomi tara kebantattu (LCDAs) na jihar.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Legas ta ce babu bukatar damuwa kan shirin aiwatar da dokar hana Okada.
Kwamishinan yada labarai da dabaru, Gbenga Omotosho, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an samar da matakan dakile duk wani hargitsi, inda ya ce za a aiwatar da dokar ba tare da wata tangarda ba.
“Babu bukatar damuwa game da aiwatar da dokar, wanda akasarin mutanen Legas ke yabawa a matsayin karfafa dokar zirga-zirgar Legas 2012 (wanda aka gyara a 2018),” in ji Kwamishinan.
Idan za a iya tunawa, a ranar 18 ga watan Mayun 2022, Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da dakatarwar a wani taro da kwamishinan ‘yan sandan jihar, da kwamandojin yankin da kuma jami’an ‘yan sanda na shiyyar a fadar gwamnati dake Alausa.
Daga ranar Laraba 1 ga watan Yuni 2022, gwamnan ya umurci jami’an tsaro da su aiwatar da dokar hana fita a fadin yankunan da abin ya shafa: Eti-Osa, Ikeja, Surulere, Lagos Island, Lagos Mainland, da Apapa.