Gwamnatin Jihar Legas, ta rufe kasuwar Oke-Afa, Isolo, da Katangua, Abule Egba, bisa karya ka’idojin zubar da shara, da suka hada da rashin tsaftar muhalli a kasuwannin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun darakta mai kula da harkokin jama’a na hukumar kula da shara ta Legas, Misis Folashade Kadiri.
- Ba Irin Wannan Amurkar Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Suke Bukata Ba
- An Kammala Bitar Wasan Kwaikwayo Karo Na Biyu Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na 2024Â
LAWMA ta ce rufe kasuwannin ya zama dole don dakile karuwar matsalolin kiwon lafiya da muhalli.
Da yake tsokaci game da lamarin, kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar, Mista Tokunbo Wahab, ya ce wani shirin gwamnati a bara da bai lamunci zubar da shara ko ina ba yana nan daram.
Ya ce gwamnatin Jihar Legas ta haramta amfani da rarraba robobin rike sanyi ko zafi da ake amfani da su don sau daya a jihar.
Kwamishinan ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar, Kunle Adeshina.
Ya kara da cewa, robobin rike sanyi ko zafi ne ke da babban kaso na sharar da Hukumar Kula da Sharar ta Jihar Legas ke mu’amala da su akai-akai da ake zubarwa a kan manyan tituna da kasuwanni.
Adeshina, ya yi nuni da cewa, ya kamata hukumar yaki da rashin da’a da hukumar kula da sharar ta jihar su dakatar da ayyukan duk wani kamfani da ke kera robobin da kuma kamfanonin rarrabawa da ke cikin jihar domin kaucewa ci gaba da rabawa.