Gwamna Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya jagoranci sayar sa takin zamani ga manoma kan farashin Naira 12,000.
Gwamnan ya ce; “Kudurin bunkasa harkar noma domin samar da abinci mai yawa a kasa. Shi ya sa muka ga cancantar samar da takin zamani a kan lokaci.
- Xi Ya Tayawa Azali Assoumani Murnar Sake Zaben Shugaban Comoros Ta Wayar Tarho
- ‘Yansanda Ne Ke Bayar Da Babbar Gudunmuwar Satar Mutane A Nijeriya – Seun Kuti
“Jihar Nasarawa Allah ya albarkace ta da manyan kamfanoni na moma kamar irin su Dangote da ke bunkasa noma mai yawa a Jihar Nasarawa domin samar da su ga da sauransu.
“Jihar Nasarawa Allah ya ba mu wurare da komai muka shuka zai yi amfani. Yanzu haka wannan shirin na bunkasa noma, gwamnatin Jihar Nasarawa ta samar da taki kan farashi Naira 12,000, a madadin Naira 21,000 da gwamnatin ta sayo.”
Ya ce; “Bukatarmu mu ga taki ya shiga hannun manoma da ke noma a Jihar Nasarawa lungu da sako.”
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta biya tallafi ga ma’aikatan kananan hukumomi kamar yadda aka yi alkawari.
Gwamnan Abdullahi Sule ya bayyana haka ne wajen kaddamar da sayar da takin zamani ga manoman Jihar Nasarawa.
Bikin da ya gudana ranar Talata a harabar Nasarawa State Agricultural Diploment Programs.
Shi ma a nasa jawabin Sarkin Lafia mai Shari’a Sidi Dauda Bage ya yi godiya da Allah ya bai wa Jihar Nasarawa shugabannin masu kulawa da damuwarsu.
Ya ce; “Sanin damuwar al’umman Jihar Nasarawa da Gwamna Abdullahi Sule ke yi, yanzu jihar tana zaune lafiya komai na tafiya yadda ya dace.”