Gwamnatin jihar Neja za ta kashe Naira Tiriliyan daya cikin shekaru biyu domin bunkasa ababen more rayuwa a jihar.
Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana hakan a lokacin wani taro da aka gudanar a gidan gwamnatin da ke Minna domin fara aikin hanyar Minna zuwa Bida da Bankin Raya Musulunci (IsDB) da Asusun tallafi na Abu Dhabi (ADFD) suka dauki nauyi.
Gwamnan ya bayyana jihar Neja a matsayin mahada wacce ta hada yankin Arewa da Kudancin kasar nan, ya tabbatar da cewa, inganta ababen more rayuwa na jihar zai amfanar matuka ga jihar da kasa baki daya.
Ya kuma yabawa Bankin ISDB da ADFD bisa amincewar da suka yi na daukar nauyin aikin hanyar Minna zuwa Bida.