Ministan harkokin tattalin arziki na kasar Netherlands Vincent Karremans ya fada a yau Laraba cewa, ana ci gaba da shirin dakatar da nuna ikon gwamnati a kan kamfanin kera na’urar sarrafa lantarkin kayayyakin fasahar zamani, watau “semiconductor” na Nexperia.
Karremans ya shiga dumu-dumu cikin ayyukan kamfanin Nexperia, wanda ya kasance wani reshe na kamfanin Wingtech na kasar Sin da ke ketare, a karshen watan Satumba, a bisa hujjar gibin da aka samu na shugabanci da aka yi zargin kamfanin ya yi fama da shi.
Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana a ranar 1 ga watan Nuwamba cewa, tsoma bakin da gwamnatin kasar Netherlands ta yi a harkokin cikin gida na kamfanin ya haifar da rudanin da ake fama da shi a masana’antar kera wannan na’urar da kuma tsarin samar da kayayyaki a duniya. Kasar Sin ta bukaci kasar Netherlands da ta dauki kwararan matakai don maido da kwanciyar hankali a tsarin samar da na’urar ta “semiconductor” a duniya.
Karremans ya yi bayanin cewa, a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata gwamnatin Netherlands ta gudanar da wani muhimmin taro da mahukuntan kasar Sin. Ya yaba da matakan da hukumomin kasar Sin suka riga suka dauka na tabbatar da samar da kayayyakin fasahar sadarwa na “Chips” zuwa Turai da kuma sauran kasashen duniya.
A nata bangare ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da cewa, kasar Sin tana maraba da matakin da bangaren Netherlands ya dauka na dakatarda nuna iko a kamfanin Nexperia. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














