Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnatin tarayya na yin namijin kokari wajen yaki da kalubalen tsaro da ke addabar Nijeriya.
Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a ranar Talata a gidan talabijin na Channels, inda ya ce mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da ministan tsaro, Mohammed Badaru da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, ba sa runtsawa saboda matsalar tsaron kasar nan.
- Sin Ta Kafa Tsarin Ilimin Koyar Da Sana’o’i Mafi Girma A Duniya
- Mutfwang Ya Amince Da Mafi Karancin Albashi Na N70,000 Ga Ma’aikatan Filato
“Ba wanda yake hutawa a tsakanin, Malam Nuhu Ribadu da ministan tsaro da shugaban hafsan tsaro da kuma shugaban hukumar farin kaya (DSS).
“Ba wanda yake barci, muna aiki tukuru. Wannan batu na tsaro babban al’amari ne da ya shafi kasa baki daya, kuma ba zan zauna a nan na ki sauke nauyin tsaron ‘yan Nijeriya a madadin shugaban kasa ba,” in ji Ministan.
A cewarsa, an samu ingantuwar tsaro a kasar nan tun bayan hawan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ya kara da cewa sojoji sun durkusar da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a yankin arewa maso gabas.
Ya kuma yi nuni da cewa gwamnati mai ci ta kasance abun misali wajen tabbatar da tsaro da rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
Ministan wanda ya yi la’akari da harin da wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda ta kai a jihohin Sakkwato da Kebbi, ya bukaci ‘yan Nijeriya da ka da su yi wa Tinubu hukunci kan lamarin, yana mai cewa shugaban kasar na sane da kalubalen tsaro.
“Shugaban kasa yana kula da wadannan batutuwa. Ka da ku yi wa shugaban kasa hukunci, ko wannan gwamnati da wadannan mataki. Yin magana na da sauki, amma daukan mataki shi ne ke da sauri.
“Mun zo ranar 29 ga Mayu a shekarar da ta gabata, ba na son mu kawo siyasa cikin wannan. Dukanmu mun san halin da ake ciki a fadin kasar nan, shin mun isa inda muke son isa? Amsar ita ce a’a. Muna inda muka kasance? Amsar ita ce a’a. Mun samu ci gaba,” in ji Tunji-Ojo.