Gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnatin jihar Kano tallafin tirela 100 na shinkafa da tirela 44 na dawa da kuma tirelar masara hudu don rabawa mabukata a jihar.
Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi a Kano.
- Yadda Dangote Ke Ciyar Da Mutum 10,000 Kullum A Kano Baya Ga Buhun Shinkafa Miliyan 1 Da Ya Raba
- Ramadan: ‘Yan Kasuwa Sun Koka Kan Samun Ƙarancin Ciniki A Kano
Ya ce gidauniyar Dangote ta kuma tallafa wa jihar da buhunan shinkafa 10,000 120,000.
“Baya ga wannan tallafin, gwamnatin jihar ta bayar da tirela 145 na hatsi iri-iri domin rabawa ga kananan hukumomi 44 da mazabu 484,” inji shi.
Tofa ya ce sun yi hakan ne tare da hadin guiwar kananan hukumomin jihar.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma fara gudanar da bincike kan shirin ciyarwa na watan Ramadan da ake yi a jihar.
Tofa ya ce Gwamna Abba Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda shirin ke gudana a lokacin da ya kai ziyarar ba-zata zuwa wasu zababbun cibiyoyin ciyarwar azumin da ke cikin birnin Kano.
” Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa da abin da ya gani a cibiyoyin, inda ya yi tambayoyi da dama wadanda ba su da amsoshi daga masu gudanar da aikin abincin.
“Gwamnan ya ce nan da sa’o’i 24 masu zuwa, gwamnati za ta sake tsara kwamitin ciyar da abinci don gudanar da aikin,” in ji shi.
Tofa ya ce gwamnatin jihar ta kebe cibiyoyi 80 na ciyar da abinci a kananan hukumomi takwas, kuma manufar ita ce ciyar da mutane 1,000 a kowace cibiya.
“Yusuf ya ziyarci wasu cibiyoyin da ke aikin ciyar da abincin, ya ga abin da ke faruwa, inda ya tarar da sabanin abunda suka tsara na ciyar da mutane 1,000 da aka yi niyya a kullum, sai suka samu mutane 450 ne kadai ke cin gajiyar ciyarwar a cibiyoyin da ya ziyarta,” inji shi.
Tofa ya ce saboda halin da ake ciki a cibiyoyin, gwamnan ya ba da umarnin sake tsara kwamitin da zai tafiyar da aikin.
Ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike kan dukkan masu hannu a ciki don hukunta wadanda aka kama da aikata laifi a aikin ciyarwar.