Matashin mawakin gambara dan asalin Zaria da ke Jihar Kaduna, Mubarak Abdulkarim wanda aka fi sani da 442 a wata hira da yayi da jarumar Kannywood Hadiza Gabon a cikin shirinta na Gabon’s Room Talk Show ya bayyana yadda gwamnatin Nijeriya ta nuna halin ko in kula a kan tsare shi da aka yi a kasar Nijar bayan samunsa da laifin yin biza ba bisa ka’ida ba.
442 ya tabbatar da cewar duk da cewar wasu ‘yan kasar Nijar ne suka damfareshi wajen nema masa bizar zama a kasar da ke yammacin Afirika, inda daga baya suka gudu bayan sun gano cewar hukuma tana bincike a kan lamarin, hakan bai sa gwamnatin Nijeriya ta hannun ofishin jakadancin kasar da ke kasar Nijar su saka baki wajen nema masu ‘yanci ba.
- ‘Yan Boko Haram Sun Sake Lalata Layukan Wutar Lantarki Mai Karfin 330KVA A Yobe
- Kwalliya A Cikin Gida
‘’Haka nan dai muka ci gaba da gwagwarmaya da sauran yan uwa da masoya wajen ganin mun shaki iskar ‘yanci bayan shafe watanni a tsare a gidan gyaran hali a kasar Nijar’’ inji 442.
Da yake amsa tambaya a kan ko ya rabu da abokiyar aikinsa Safara’u wadda aka sansu tare kafin ya hadu da wannan iftila’i a kasar Nijar, Mubarak ya tabbatar da cewa ko kusa ba shida wata matsala da Safara’u illa dai yanzu kowa a cikinsu ya kama wata sabgar wadda yake ganin ta fiye masa.
Amma a kowane lokaci na bukaci in yi aiki da ita kokuma ita da kanta ta bukaci ta dawo wajena kofa a bude take domin in amshe ta mu ci gaba daga inda muka tsaya, saboda naga cewar tanada fasahar waka kuma tana da sha’awar yin aiki tare dani inda take samun goyon bayan iyayenta.
442 ya kara da cewar har yanzu da yake wannan maganar bai yi danasanin aikata abinda ya janyo aka daureshi a gidan gyaran hali na kasar Nijar ba, domin kuwa aiki ne ya kai shi kuma wannan ce hanyar neman abincinsa kuma kowa zai iya fuskantar kalubale a kan hanyarsa ta neman abinci.
Daga karshe Mubarak ya bukaci mutane masu yi masa kallon wani wanda yake bata tarbiyar matasa ta hanyar wakokinsa da su daina aibata abinda yake yi illa dai su dinga yi masa addu’a su kuma bashi shawara idan sunga wani kuskure domin ko kadan bashida wata manufa ta bata tarbiyar matasa.