Ranar talata ne gwamnatin jihar Ondo ta tabbatar da rasuwar wasu mabiya addinin kirista su 22 a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a Cocin .St. Francis Catholic da ke a garin Owo.
Tuni gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, ya yi tir da kai harin inda ya danganta harin a matsayin harin Shedanu.
- Zaben APC: Ɗaya Daga Cikin Deliget Daga Jihar Jigawa Ya Rasu A Abuja
- ‘Yan Boko Haram Sun Yi Garkuwa Da Matafiya Da Yawa A Borno
Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar, Dakta Banji Ajaka, ya bayyana cewa akalla mutane 18 na kwance a asibitin tarayya da kuma Asibitin St. Louis da ke a garin Owo ana duba lafiyarsu.
Ya ci gaba da cewa, kimanin mutum bakwai aka yi wa magani a Asibitin St. Louis sai kuma mutum hudu da suma aka suke karbar magani da aka kuma sallame su, yanzu haka ana ci gaba da duba lafiyar mutane 19