Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayar da gudummawar kudi naira miliyan 20 ga iyalan wadanda harin bam ya rutsa da su a ranar Laraba a jihar Sakkwato.
An bayyana hakan ne a lokacin da manyan shugabannin siyasa a jihar suka isa karamar hukumar Silame domin halartar jana’izar wadanda sojoji suka harba wa bama-bamai bisa kuskure yayin farmakar Lakurawa dake ta’addanci a yankin.
- Boko Haram Sun Kashe Mutum 2, Sun Jikkata 3 A Borno
- Tinubu Ya Yi Wa Gwamnan Jigawa Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa
Gwamna Aliyu tare da rakiyar Sanata Aliyu Magatakardan Wamakko da kuma ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Muhammadu Maigari Dingyadi, duk sun samu halartar sallar jana’izar wadanda lamarin ya rutsa da su.
Da yake bayyana lamarin a matsayin abin takaici, Gwamna Aliyu ya jajanta wa al’umma tare da danganta lamarin da kaddarar Ubangiji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp