Sharifiddeen sidi Umar" />

Gwamnatin Sakkwato Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibin Da Aka Sare Wa Hannu Biyu

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta dauki nauyin karatun matashin dalibin jami’a Habibu Abu Atto Nakasari wanda wasu bata gari suka sarewa hannu biyu bakidaya.
Gwamna Tambuwal ne ya bayyana hakan a yayin da ya ziyarci maras lafiyar a asibitin kashi da ke Wamakko tare da nuna jimami da alhinin faruwar lamarin wanda ya girgiza daukacin al’umma.
Gwamnan ya bayyana cewar wajibi ne a hukunta wadanda suka aikata aika-aikar domin kamar yadda ya bayyana Gwamnatin Jiha da hadin guiwar Hukumomin Tsaro suna iyakar kokari domin ganin an kama tare da hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.
Tambuwal ya kuma bayyana cewar Gwamnatinsa za ta dauki nauyin jinyar matashin bakidaya tare da daukar nauyin karatunsa tare da bashi aikin yi bayan ya kammala karatu.
Matashi Habibu A. Nakasari wanda dalibin Nazarin Harshen Turanci ne a Jami’ar Usmanu Dan- Fodiyo ya hadu da tsautsayi ne a makon jiya ta yadda wasu ‘yan ta’adda a cikin dare suka sare masa hannu biyu bakidaya.
Rahotanni sun bayyana cewar an kaiwa Habibu farmaki ne da misalin karfe biyu na dare a unguwar Mana da ke a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu a inda suka gutsure masa hannaye biyu tare da tserewa da mashin dinsa.
Tambuwal ya kuma jaddada cewar Gwamnatinsa ba za ta taba goyon bayan kowane irin nau’in ayyukan ta’addanci ba a Jihar domin Gwamnatinsa Gwamnati ce wadda ta nesanta ga ayyukan ta’addanci tare da karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.
Ita kanta jami’ar Usmanu Dan-Fodiyo ta bayyana cewar za ta dauki mataki na musamman domin ganin karatun dalibin bai lalace ba kamar yadda Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya bayyana tare da cewar za su fito da tsare-tsaren da dalibai masu ire-iren wannan matsalar za su iya karatu ba tare da wata matsala ba.
Idan za a iya tunawa dai a makwannin da suka gabata, wani matashi daban Abdullahi Shehu ya hadu da irin wannan jarabawar jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben ta yadda wasu matasa da ake zargin ‘yan jam’iyyar adawa ne suka sare masa hannu wanda Gwamna Tambuwal ya daukar masa shatar jirgi zuwa Abuja domin ganin ko za a iya mayar da hannun amma lamarin ya faskara.

Exit mobile version