Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar da shirin sa yara da suka isa shiga makaranta na shekarar karatu ta 2024/2025 wanda aka shirya shi ne domin duk yaran da shekaraunsu sun kai su shiga makaranta an sa, su a makarantun gwamnati.
Da yak e jawabi wajen kaddamar lokacin da aka kaddamar da tsarin wanda aka yi a amakarantar Firamaren a ‘ya’yan sojoji Kwannawa, cikin karamar hukmar Dange Shuni, Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewar ita maganar daukar yara da sa su makaranta na daya daga dikin tsare- tsaren na matakan da gwamnati ta dauka a wani kokarin da take yi na, gano yaran da basu zuwa makaranta,da suka hada da wadanda ba a taba sa su makaranta ba, da kuma wadanda aka sa su amma yanzu ba su zuwa.
- Sin Ta Goyi Bayan Kudurin Kafa Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta AU A Somaliya
- Bunkasar Tattalin Arzikin Sin Ta Kawo Damammaki Ga Duniya
Da yake jawabi kan irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu ta bangaren ilimi, gwamnan yace, “shekarar data gabata, gwamnatin Jihar ta hanyar hadin gwiwa da ma’aikatar ilimi ta tarayya sun kafa makarantiu uku na karamar Sakandare a mazabu uku na ‘yan majalisar dattawa,wadanda aka kaddamar a watan Mayu na shekarar 2024 wadda karamar Ministan ilimi, Dakta Yusuf Tanko Sununu yayi.
Ya ce“Sun biya Naira miliyan 150,000,000 a matsayin kudin da gwamnatin Jiha rya dace ta bada da kuma Naira miliyan 50,000,000 saboda a fara aiwatar da tsarin AGILE a Jihar har ma da gina azuzuwa 147,da kuma gyara 142, samar da wuraren Bahaya / Masai na zamani 208, zagaye makarantu da katanga, da rijiyoyin burtsatse, duk wannan domin a samar da yanayi maikyau saboda a ji dadin koyarwa suma wadanda ake koya mawa su ji dadin hakan.
“An yi horo da sake horar da Malaman makaranta a kananan hukumomi 23 na Jihar saboda a samu bunkasa iliminsu da kwazon aikinsu.Hakanan ma an sayo saitin kayayyakin karatu 9,852 saboda Malami da ‘yan makaranta, har ma da samar da wadansu abubuwan da makarantu ke bukata.
“Wannan ya hada da lamarin sake farfado da ciyar da yara abinci a makarantun kwana 23 da suke da dalibai 17,367, ana amfani da Naira miliyan 680,786,400 kowace shekara.Tsarin ciyarwar ya hada da makarantun Firamare uku da ake kwana.
“An dauki sabbin Malamai 2,000 wadanda aka tura su, su koyar a makarantun Sakandare na ‘ya’yan Fulani a fadin Jihar. Bugu da kari mun gabatar da bada Naira 200,000 ga dukkan makarantun Sakandare saboda a rika yin dan karamin gyara na wadansu abubuwan aiki a cikin makaranta.
Ya kara jaddada cewa “Bada dadewa bane suka bada kwangilar sake gyaran gaba daya na makarantun Sakandare dana Firamare na Jihar.”
Da yake karin haske kan kudurin da gwamnatinsa take da shi dangane da bunkasa ilimi fiye da yadda ya same shi, Gwamna Aliyu ya yi kira da iyaye da kuma wadanda alhakin ilimin yaray a rataya a wuyansu a Jihar, da su ba gwamnatinsa goyon baya wajen tabbatar da cewar ‘ya’yansu suna zuwa makaranta kullum kamar yadda ya kamata.