Gwamnatin Jihar Sakkwato ta fara shirin sayar da shinkafa da sauran kayayyakin abinci, inda za ta sayar da su da ragowar kashi 55 na kayan da ta sayo na Naira biliyan 14.
Gwamna Ahmed Aliyu ne, ya sanar da hakan a lokacin da yake kaddamar da kwamitin bibiya da sa ido a kan sayar da kayan abinci a ranar Litinin.
- Ban Ji Dadin Abin Da Libya Ta Yi Wa Super Eagles Ba – Tinubu
- NNPP Ta Dakatar Da Sakataren Gwamnatin Kano Da Kwamishinan Sufuri
Gwamnan, ya ce sun dauki matakin ne domin rage wa mutane radadin da suke ciki na matsin rayuwa tun bayan cire tallafin man fetur.
Kazalika, ya ce abincin zai kai dukkanin mazabun jihar guda 244.
“Ku guji sanya bambancin siyasa ko addini wajen sayar da kayayyakin abincin. Wannan abinci ne na dukkanin jama’ar Sakkwato,” a cewarsa.
Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da tallafi irin haka har zuwa lokacin da tattalin arzikin kasar zai bunkasa.
Sannan ya yi kira ga masu hannu da shuni da kamfanoni a jihar, da su taimaka wajen rage wa mutane halin da suke ciki.