Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi alƙawarin tallafa wa ‘yan kasuwar da gobarar da ta shafa a Kasuwar Kara.
Gobarar ta ƙone shaguna 50, injinan niƙa 132, da kayan abinci da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Wasu Sassa A Makkah
- Kasar Habasha Ta Jinjina Wa Kamfanin Kasar Sin Bisa Kirkiro Da Ayyukan Yi a Kasar
Mataimakin Gwamnan Jihar, Idris Mohammed Gobir, yayin ziyarar da ya kai wajen da abin ya faru, ya bayyana cewa gwamnati za ta kafa kwamitin da zai tantance asarar da aka yi tare da samar da hanyoyin kaucewa irin wannan matsala a gaba.
Ya kuma yi kira ga jama’a su kula musamman a lokacin hunturu.
‘Yan kasuwar sun yi godiya ga kulawar gwamnatin tare da roƙon a taimaka musu cikin gaggawa, ganin yadda gobarar ta yi tasiri ga kasuwancinsu da rayuwarsu.