Gwamnatin Jihar Sakkwato, za ta fitar da Naira miliyan 95.4 domin gyaran Masallatan Juma’a 87 da ke fadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bello Goroyo ne, ya bayyana hakan a Cibiyar koyar da Alkur’ani da Addinin Musulunci ta Sultan Muhammad Mccido a ranar Laraba.
- Boko Haram Sun Sake Kai Wani Hari Kan Al’ummar Kirawa A Jihar Borno
- A Dawo Da Tsohon Farashin Man Fetur Cikin Gaggawa – NLC
Ya ce an raba Masallatan zuwa kashi uku, 20 daga ciki sun samu kudin gyara da ya kai Naira 500,000, wasu 17 kuma sun samu naira 400,000, sai wasu huda 50 da suka samu Naira 300,000 a matsayin kudin gyaran.
Goronyo, ya bayyana cewa kudin da aka ware na watannin Agusta da Satumba da kuma Oktoba ne, an kuma samu tsaikon tura kudin sakamakon wasu daga cikin Masallatan ba su da asusun ajiya a banki har sai da aka bude musu.
Ya kara da cewa tuni aka bayar da kudaden kuma hakan wani bagare ne na cika alkawarin da gwamnan ya dauka a lokcin yakin neman zabe na ingata wuraren ibada.
Kudaden na daga cikin alawus din da gwamnati ke bayarwa domin gyaran Masallatai a kowane watanni uku.
Idan ba a manta ba gwamnatin ta sha suka a baya-bayan kan makudan kudaden da ta cire wajen gyada burtsaten ruwa guda 25 a jihar.