Gwamnatin Jihar Sokoto ta ba da tabbacin tallafa wa waɗanda gobarar kasuwar Kara ta rutsa da su, tare da miƙa saƙon jaje ga ‘yan kasuwar da suka yi asara a gobarar.
Gobarar da ta tashi a kasuwar ta ƙone shaguna kimanin 50, ta lalata injinan niƙa guda 132 da kayan abinci irinsu shinkafa, da gero, da wake, waɗanda aka ƙiyasta sun kai miliyoyin Naira.
- Sokoto Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 15 Ga Gyaran Makarantu, Motocin Alkalai Da Sauransu
- Tashin Hankali: Gobara Ta Yi Sanadin Rasuwar ‘Yar SSG Na Sokoto Da ‘Ya’yanta 3
Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Idris Mohammed Gobir, ya kai ziyara kasuwar domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa. Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta kafa kwamiti don tantance girman asarar da kuma nemo hanyoyin kare aukuwar irin wannan gobara nan gaba.
Gobir ya ja hankalin jama’a kan kula da dabarun kare kai daga gobara, musamman a lokacin hunturu, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ba da tallafi bayan kammala rahoton kwamitin. Shugaban ƙungiyar masu Injin Niƙa, Malam Yakubu Bello, ya tabbatar da girman asarar da aka tafka, yayin da Shugaban ƙungiyar Matasa ‘Yan kasuwa, Alhaji Bashar Nuhu, ya nemi tallafin gwamnati, yana mai cewa matasa sun fi jin zafin wannan ibtila’in.